<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Yesu Mai Ceto, ni ya ke so,
 Mai pansata ne mai taimako.
 Ya sha azaha don laifina,
 Ya ba ni rai na har abada.

[V2]
 KORUS
 Yesu Ɗan Allah shi na ke bi
 Har za ya komo ya fyauce ni.

[V3]
 2) Yesu Mai Ceto, ka ƴanta ni
 Daga bauta ta zunubaina.
 Cika zuciya da ƙaunarka,
 Kada in ƙara son duniya.
 Korus

[V4]
 3) &quot;In za ka bi ni.&quot; Yesu ya ce,
 &quot;Bar neman kome, sai ni kaɗai.
 Wanda ya ɗauki giciyensa
 Ba za ya rasa ladansa ba.&quot;
 Korus

[V5]
 4) Tun da na zama masoyinsa,
 Ba na jin tsoron mutuwa dai.
 Gama, in ji shi, zai koma can
 Ya shirya wurin zamanmu duk.
 Korus</lyrics>
<title>Yesu Mai Ceto, Ni Ya Ke So LW216</title>
<hymn_number>216</hymn_number>
</song>